Labarai

Tsige Sunusi: Zanyi mamaki idan da Buhari ya sa baki mukai ga abinda ya faru – Gen Abdussalam

Tsohon shugaban Najeriya, Janaral Abdussalam Abubakar, ya bayyana rashin jin dadinshi bisa tsige Sarki mai murabus na Kano, Mallam Muhammadu Sunusi na 2 daga mulkin Kano.

DABO FM ta tattara cewar a jiya Litinin ne dai gwamnatin Kano karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Mallam Sunusi tare da maye gurbinshi da Alhaji Aminu Ado Bayero cikin sa’o’i kadan.

Janaral Abdussalam ya bayyana shakkunshi akan rashin saka bakin shugaba Muhammadu Buhari a cikin rikicin, inda ya bayyana cewar in har shugaban ya sanya baki, to lallai akwai mamakin jin tsigewar Sarkin.

Yayin wata ganawa da tsohon shugaban yayi da sashin Hausa na Muryar Amurka, ya bayyana tsige Sarkin a matsayin abin bakin ciki.

“Abinda zance Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, wannan labari ne mummuna, muna fata Allah Ya kauda fitina a Kano bisa wannan abinda akayi.”

“Allah ya gani, munyi iyakacin kokarinmu, mu zauna da gwamna da Sarki, mun kuma basu shawarwarin abinda mu mukaga yakamata ayi, bayan mun gama aikin munga alama”

Da yake amsa tambayar, ko shugaba Buhari ya sanya baki acikin rikicin da yake tsakaninsu?

“To a halin yanzu bazan iya cewa ko shugaba Buhari yasa baki a wannan magana ko bai sa ba domin bana Najeriya, amma kafin in taso lokacin da muka mika masa bayanan da muka tattara, mun tattauna dashi kuma ya nuna zai sa baki don a samu masalaha, to bayannan ko ya samu yayin magana, ban sani ba.”

DABO FM ta tattara cewar tsohon shugaban ya sake amsa tambayar kan cewar ko rashin sanya bakin shugaba Buhari ne ya kai ga tsige Sarki mai murabus?

“Bansani ba ko yasa baki ko bai sa ba, amma da alama yasa baki din tinda ya karbi rahoton bincikenmu, da alama yasa baki amma bazan iya tabbatarwa ba.”

“Kuma in yasa baki, zanyi mamaki bayan yasa baki mu kai inda wannan abu ya faru, amma kasan komai sa baki da shawarar wani abinda Allah ya kaddara, babu mai canza shi.

UA-131299779-2