Labarai

Kaci gaba da zama mutum mai juriya kamar yadda Allah yayi ka – Dan Kwambo ga Sanusi II Murabus

Ibrahim Hassan Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Gwambe yayi kira ga Sanusi II Murabus da yaci gaba da kasancewa mutum mai juriya kamar yadda Allah yayi shi mutum jajirtacce kuma mai juriya.

Majiyar Dabo FM ta rawaito tsohon gwamnan na fadin hakan ne a yammacin Litinin bayan sauke sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar Kano tayi karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje.

Cikin sakon alhini da Dankwambo ya fitar ya ce “Kada ka taba bari wani yanayi na rashin jin dadi ya bayyanar da bacin ranka, ka ci gaba da bayyanar da kyawawan halayen ka da juriya kamar yadda Allah ya halicce ka da ita.”

Ya kara da cewa “Bazai yiyu arewa taci gaba da zama a haka ba wanda kullum muna kara kashe kanmu.”

UA-131299779-2