Labarai

Jami’ar UNIZIK zata bawa Sarki mai murabus Sunusi Lamido digirin girmamawa

Jami’ar Nmadi Azikwe dake garin Akwa na jihar Anambra ta ayyana Sarkin Kano murbus, Mallam Muhammadu Sunusi II daga cikin wadanda zata baiwa digirin girmamawa.

Hakan yazo ne jim kadan bayan tsige Sarkin da gwamnatin jihar Kano tayi.

DABO FM ta tattara cewar shugaban jami’ar, Farfesa Charles Esimone ne ya bayar da sanarwar a jiya Litinin, ya kuma bayyana za a gudanar da taron a tsakanin 9 da 13 na watan Maris da muke ciki.

Sarkin Kano murabus, Muhammadu Sunusi na 2 da shugaban kamfanin motocin INNOSON, Innocent Chukwuma da sauran wasu mutane ne zasu karbi digirin na girmamawa a yayin taron yaye dalibai na makarantar.

Tini dai aka maye gurbin Mallam Muhammadu Sunusi da dan uwanshi, Alhaji Aminu Ado Bayero tare da nada Alhaji Nasiru Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Bichi.

UA-131299779-2