Tsohon Alƙalin alƙalan jihar Kano, Jastis Shehu Atiku ya rasu yau Lahadi 27 ga Satumba.
Dabo FM ta samu wannan sanarwa daga bakin kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim a daren Lahadi.
Rahoton ya kuma bayyana za’ayi jana’izar sa gobe Litinin 10 na safe a gidan sa dake kan titin Sokoto Road, Justis Shehu Atiku ya yi ritaya a Junairun 2015.