(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Da dumi-dumi: Boko Haram sun sake afka wa tawagar Gwamna Zulum, karo na 3

Karatun minti 1

Mayakan ta’addanci na kungiyar Boko Haram sun sake afka wa tawagar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da safiyar yau Lahadi.

Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan mayakan kungiyar sun afka wa tawagar gwamnan, lamarin da ya kai ga mutuwar jami’an tsaro 26 da farar hula 4.

Sai dai rahotanni sun ce ba a rasa rai a wannan hari da Boko Haram  suka kai wa gwamnan ba.

PUNCH ta tattara cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 10:30 na safiyar yau Lahadi a kusa da garin Baga, nisan da bai gaza kilomita 2 ba.

Wani daga cikin wadanda suka samu rauni yayin faruwar al’marin sun ce mayakan kungiyar  ta’addanci ta Boko Haram ne.

Wani daga cikinsu masu raunin ya ce: “Babu wanda ya rasa ranshi sai dai kananun ciwuka.”

“An farfasa gilasan wasu motoci, wasu motoci an farfasa tayoyinsu da harbi, ciki har da motar tawagar masu yada labaran gwamnatin jihar.”

“An hahharbi motar sojoji, kafadar wani soja ta kone sakamakon harbin bindiga.”

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog