(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Wani mutum ya kwarara wa wasu matasa 8 ruwan batir a jihar Anambra

dakikun karantawa

A kasuwar Ugwuagba ta jihar Anambra ne dai aka samu wani mutum ya shekawa wasu mutane guda 8 ruwan batiri, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Jaridar tace majiyar data bayyana mata labari tace; bayan mutumin ya aikata wannan mumunar aiki ya cikawa wa wandonsa iska ya gudu.

“ Mutumin ya aikata haka ne a dalilin ‘yar gadama da ya hadashi da wani abokinsa mai suna Onyeka dake siyar da kayan mota a kasuwar.

Su ma a nasu bangaren, rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun kakakinta na jihar DSP Haruna Muhammad, ta tabbatar da faruwar wannan al’amarin, sai dai ya bayyana cewa har yanzu babu wanda hukumar ta cafke.

“ Mun samu labarin cewa wani ya kwarara wa abokinsa Onyeka Nwachukwu mai shekaru 38 ruwan batir a dalilin gaddamar daya auku a tsakanin su.

“Sai dai kuma ba shi kadai ruwan batir din ya yi wa ta’adi ba domin ya illata wasu mutane bakwai dake kusa da wurin da rikicin ya barke bayan shi wanda aka duldulawa.” – Fassarar Sashin Hausa na Premium Times

Kakakin yan sandan yace tini dai suka aike da mutane 7 zuwa asibitin ‘Martin’ na unguwar Ugwuagba, domin karbar agajin gaggawa inda ya shaida cewa daga bisani asibitin ya sallami mutane 6 daga ciki.

Ya kara da cewa, hukumar dai ta bazama domin kamo wadanda suke da hannun a cikin mummunar ta’asar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog