(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kamfanin tafiye-tafiye ya tabbatar da bawa dalibar ‘Abba Gida Gida’ kujerar Umara

Karatun minti 1

Rade-radin da yake bazuwa a kunnuwan al’umma na samun kyuatar kujerar Umara da dalibar nan Rafi’atu ta samu daga wani kamfanin shirya tafiye-tafiye a jihar Kano.

Hakan yasa DABO FM ta tuntubi kamfanin dake da zama a kan titin Ahmadu Bello na jihar Kano don jin ta bakin su.

DABO FM ta zanta da Nura Ado Yakasai, mataimakin mai gudanarwar kamafanin IBRANTA Travels & Tours ya tabbatar mana da cewa lallai sunyi wa wannan daliba alkawarin kujerar Umara.

Nura Yakasai ya kara tabbatar wa DABO FM cewa shugaban kamfanin, Jibrin Muhammad, ne ya tabbatar da baiwa Rafi’a kyautar zuwa Umara.

“Maganar da akeyi akan biyawa wannan dalibar kujerar Umara gaskiya ne.”

“Mutane da yawa sun kira ni jiya akan wannan maganar, kuma shi shugaban kamfanin, Jibrin Muhammad, ya tabbatar min shine yayi mata alkawari kuma babu haufi a ciki.” – Nura Yakasai.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog