Labarai

Sabbin Sanatoci sun raina albashi da alawus na miliyan 14 da suka karba a watan Yuni

Bulaliyar majalissar dattijai, Sanata Orji Uzor Kalu na jihar Abia, ya bayyana cewa wasu daga cikin Sanatoci sun shiga cikin yi masa korafi akan albashin da aka basu a watan Yuni.

Sanata Orji yace; Sanatocin sunce ba haka sukayi tsammani za’a basu ba kafin zabe.

Gidan Talabijin na OAK TV ya rawaito cewa Sanata Orji ya bayyana haka ne a babban birnin tarayyar Abuja ya kuma bada tabbacin nan bada dadewa ba zai fito ya bayyana ainahin abinda Sanatocin suke samu.

Orji yace albashin da kafafen yada labarai suke rubutawa ana baiwa Sanatocin ba gaskiya bane inda ya bayyana cewa abinda ya karba a watan Yuni yayi kasa da abinda aka saba rawaito wa.

“Abunda kuke kira albashi mai tsoka sune kudaden da muke amfani da shi wajen gudanar da ayyuka a mazaba saboda basu bamu karin kudade. Kudin ne muke amfani da shi idan zamu yi tafiya zuwa Abia, Legas, ko Kaduna.”

Zuwa nan gaba zan bayyana muku, zaku ga cewa korafin da akeyi a kan yan Majalisar Dattawa suna karbar kudade na banza ne.”

A baya bayan nan ne dai manyan jaridun kasa suka rawaici albashi da alawus na Naira miliyan ‭14,330,000‬ da kowanne Sanata a Najeriya yake karba a kowanne wata.

Shima tsohon Sanata da ya fito daga jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyana hakikanin kudaden da ake baiwa kowanne sanata a wata wanda ya bada tabbacin abinda jaridun kasa suka fada gaskiya ne.

Karin Labarai

Masu Alaka

Akwai yiwuwar samun sabuwar Boko Haram idan ba’a saki Sheikh Zakzaky ba – Majalissar tarayya

Dabo Online

Bayan suka da cece-kuce, Ahmad Lawan ya janye mukamin daya baiwa tsohon ma’aikacin Saraki

Dabo Online

Majalissar Dattijai ta tabbatar da Tanko Muhammad a matsayin Alkalin Alkalai

Dabo Online

Ali Ndume ya taya Sanata Ahmad Lawan murnar lashe zaben shugaban majalissar Dattijai

Dabo Online

Karin Albashi: Majalissar Dattijai ta amince da karin albashin N30,000

Dangalan Muhammad Aliyu

Majalissar Dattijai ta fara tantance sunayen Ministoci

Dabo Online
UA-131299779-2