(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Yan Bindiga sun sake harar wata makaranta a Kagara, sun sace mutum 7

Karatun minti 1

Yan bindiga sun sake koma wa garin Kagara da ke jihar Neja a Najeriya, sun sace mutum 7.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun afka makarantar GTC Kagara da ke karamar hukumar Rafi a jihar ta Neja, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar cewar yan bindigar sun afka makarantar ne da tsakar daren Asabar, sai dai basu iske kowa ba.

Hakan na zuwa bayan da gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar bayan sace dalibai GSS Kagara a makon da ya gabata.

Yan bindigar sun fita daga makarantar cikin fushi domin a cewar majiyoyin, yan bindigar su na neman mutane da yawa ne.

“Sun fita daga makarantar, suka nufi wani ƙauye a kusa da makarantar  in da a nan ne suka sace mutum 7.”

“Sun iske makarantar babu kowa, hatta ma’aikata a makarantar ma ba sa ciki.”

Daga cikin waɗanda aka sace sun haɗa da wani Alhaji Aminu, shugaban ruwan fiyawata na Kongwama Table Water.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog