/

Za a fara cin gyaran kafafen yaɗa labaran Hausa da ke ‘danne’ haƙƙoƙin rubutacciyar Hausa

dakikun karantawa

Wasu matasa masu amfani da shafukan sada zumunta musamman  Facebook, sun ɗaura ɗamarar kawo sauyi domin inganta rubutun Hausa.

A cewar matasan, lokaci ya yi da ya kamata a ce kafafen yaɗa labarai da suke amfani da yaren Hausa sun zama tamkar allon misali ga ɗalibai domin inganta rubutun Hausa a tsakanin al’umma.

Sai dai a cewarsu, mafi yawan kafofin yaɗa labaran suna kunyata yaren, lamarin da ya sanya suka ce za su fara ɗaura hotunan kurakuran da kafofin suke yi ko hakan zai sa su gyara.

Wani mai amfani da sunan ‘Bin Danladi Mailittafi’, ya ƙaddamar da wani shiri mai taken; ‘Gyara Gaba Gyara Kintsi’ domin fito da irin kurakuran da wasu daga cikin kafofin yaɗa labarai suke yi tare da yi musu gyara.

Ya ce; “Za mu fara ja wa rubututtukan labaran jaridu da mujallun Hausa jan layi, ko hakan zai tilasta musu kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa, su daina yin wasarere da su.”

“Abin kunya ne a ce kamar BBC Hausa, ko VOA Hausa ana samun kurakurai a jaridunsu, ba ma a ta batun kananun gidajen jaridunmu na nan gida, kwamacalar ta yi yawa.”

Shi ma wani shahararren, Ibn Magaji Alhausawi, mai koyar da Hausa a cikin wani shiri da ya ke gabatarwa mai taken ‘Gyara Kayanka’ a manhajar Facebook, ya goyi bayan shirin tare yaba wa Mailitaffi a kan fito da ƙirƙirarren shirin.

Ya ce; “Madallah da wannan yunƙuri. Allah Ya yi jagora.”

DABO FM za ta riƙa bibiyar sabon shirin domin kawo wa masu bibiyarmu don bada gudunmawarmu wajen inganta rubutun Hausa.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog