/

Shekara 14 rabon da jami’iyyar hamayyar taci zabe a zaben kananan hukumomin Kano

dakikun karantawa

JAIPUR INDIA: A makon da muke ciki ne dai aka kammala zaben kananan hukumomi a jihar Kano, zaben da ya samar da shugabannin kananun hukumomi 44 da kansiloli 484  a jihar Kano.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ‘KANSIEC’ ta sanar da jami’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe dukkanin guraben shugabancin kananun hukumomi da mazabu a jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewa mafi yawan al’ummar jihar Kano basu fita domin kada kuri’unsu a zaben ba, al’amarin da wasu ke kallo a matsayin tasirin tsagin PDP da suka ce ba za su fafata a zaben ba.

Sai dai DABO FM ta bincika cewar, ko kusa ko nesa, hukuncin jami’iyyar PDP na kin shiga zaben ba shi da alaka da rashin fitowar al’ummar Kano domin kada kuri’unsu a zaben.

Binciken DABO FM ya yi nuni da cewa al’ummar jihar sun ki fitowa ne domin fitowarsu ba ta da tasiri wajen zabe, su na ganin ko sun fito ko basu fito ba, ‘yan takarkarun jami’iyya mai mulki ta APC ne za su lashe zaben kamar yadda aka gudanar a shekarar 2014 da kuma 2018.

Binciken dai ya tabbatar da cewa an shafe shekaru 14 ba a samu wani dan jami’iyyar hamayya da ya lashe wata kujera a zaben kananun hukumomin jihar ba, tin bayan da jami’iyyar PDP ta samu nasarar lashe zabe a kananun hukumomi 3 a shekarar 2007.

Kananun hukumomin sun hada da Dawakin Kudu, Kumbotso da Warawa.

Daga baya kotu ta kwace zaben Dawakin Kudu daga hannun PDP zuwa ANPP, a karshen wa’adin mulkin shugabannin kananun hukumomin, kotu ta tabbatar da PDP a matsayin jami’iyyar da ta lashe zaben karamar hukumar Nassarawa.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog