(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zamu fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Buhari

dakikun karantawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta iya fitar da mutum miliyan 100 daga talauci idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata.

“Akwai alaka tsakanin talauci da koma bayan tattalin arziki da cin hanci da kuma rashin zaman lafiya,” a cewar shugaban, wanda ke magana a ranar bikin cika shekara 20 da kawo karshen mulkin soji a kasar. 

Shugaba Buhari, wanda ya fara wa’adi na biyu a karshen watan Mayu ya ce tun da kasashen China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya ci gaba.

Ya kara da cewa: “Kasashen China da Indonesia sun ci gaba karkashin tsarin mulkin mulukiya yayin da India ta kai gaci a karkashin tsarin demokuradiyya, a don haka muma babu abin da zai hana mu mu kai ga gaci”.

Sai dai bai yi wani cikakken bayani kan yadda gwamnati za ta yi hakan ba, abin da ya sa wasu ke ganin kalamai ne kawai irin na ‘yan siyasa da sukan yi domin birge jama’a ko jan hankalin masu sauraransu.

Najeriya ta fi kowacce kasa yawan arzikin man fetur da kuma jama’a a Afirka, amma tana sahun gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, abin da ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci.

Wannan ne karon farko da ake yin bikin Ranar Demokuradiyyar a 12 ga watan Yuni. 

An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma “rage radadin” alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.

BBC Hausa

Karin Labarai

Sabbi daga Blog