Kano: Budurwa ‘yar shekara 17 ta kashe kanta saboda mahaifinta ya saki mahaifiyar ta

dakikun karantawa

Wata budurwa, Sadiya Shehu, mai shekaru 17 , ta kashe kanta saboda barkewar sa’in sa da iyayen ta wanda takai ga mahaifin ta ya saki mahaifiyar ta.

Sadiya da suke da zama a unguwar Tudun Murtala dake karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

DABO FM ta binciko faruwar al’amarin daya faru ranar Litinin.

Ta mutu ne bayan da ta sha maganin kwari wanda aka fi sani da “Fiya-Fiya” dake ajiye a dakin mahaifiyar ta wanda suke amfani dashi wajen kashe sauro.

DABO FM ta rawaito wakilan Jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, sunga cincirundon mutane masu zuwa jaje dai dai lokacin da suka kai ziyarar shaidawa idanuwansu faruwar al’amarin.

Da yake magana, mahaifin Sadiya, Mallam Shehu A Lawan ya bayyana cewa Sadiya ta kashe kanta biyo bayan wata ‘yar matsala data taso tsakaninshi da mahaifiyarta a ranar Lahadi.

“Na samu matsala da mahaifiyar ta wanda hakan yasa bata (Sadiya) ji dadi ba. Tayi ta kuka, sai dai na ce mata komai ya wuce.”

“Na tashi da sassafe na bar Sadiya da sauran ‘yan uwanta lami lafiya, ina wajen aiki na ne, kwatsam naji kira cewa an garzaya da ita asibiti. Likitoci sunyi iya bakin kokarinsu amma Allah ya karbi ranta.”

Da yake amsa tambayar ka cewa ko Sadiya tanada wanda zai aure ta, Mallam Lawan ya tabbatar da cewa akwai wanda yake neman auren ta, magana ta karshe tsakaninsu shine yace da zarar mahaifinshi ya dawo daga kasar Saudiyya, zasu zo domin nema masa auren ta.

“Amma cikin ikon Allah, auren bazai yiwuba tinda yarinya ta bar duniya har abada.”

Malama Amina Shehu, itace mahaifiyar Sadiya, tace rikicinta da mijin nata ya samu asaline lokacin da wata Maryam, ‘yar yayan mijinta, ta rika dukan karamin kanin mamaciyar yayin da shima mijin nata ya karbi dukan kanin Sadiya.

“Maryam tazo ta fara fada da ‘da na, Daddy, tace yayi mata rashin kunya. Lokacin da mijina ya fito daga wanka, sai ya fara yi masa dukan kawo wuka, ni kuma naga bazan iya dauka ba, shine nace masa koda Daddy yayi mata laifi bai kamata yayi masa irin wannan dukan ba.

“Mijina yace min inyi shiru ni kuma nace gaskiya bazanyi ba tinda ba wanda ya tausayawa yaro. Nace idan ma ta tabbata ya zagi Maryam, ai babu inda ya koyi zagin face a danginsu.

Amina na kara da cewa, mijin nata yaji matukar haushi sosai inda ya sake ta a gaban mamaciyar (Sadiya.)

“Lokacin daya ce in fita na bar gidan, ya sake ni, Sadiya ta tsugunna kasa ta fara kuka tana rokonshi kar ya barni in tafi, saboda zasu shiga yanayi marar dadi idan na tafi.”

“Kwana daya bayan sakin nawa, na tattare kaya na na bar gidan, a lokacin na fuskanci bata cikin nutsuwa kuma da damuwa a tattare da ita. Nace mata ta kwantar da hankalinta indai akan wannan matsalar ce, ta riga ta wuce.”

“Amma kwatsam ta shige daki ta sha maganin kwari (Fiya-Fiya) ta mutu.”

DABO FM ta gano cewa tini dai aka binne Sadiya ranar Litinin bisa koyarwar addinin musulunci.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi, ya bayyana cewa rundunar ba tada masaniya game da al’amarin, sai dai tayi alkawarin yin bincike daga wajen DPO na unguwar da lamarin ya faru.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog