Ƙwacen waya a Kano, Daga Mubarak Ibrahim Lawan

dakikun karantawa

Mubarak Ibrahim Lawan

Kwacen Wayar Salula a Kano (I)

Kwacen wayar salula a Kano matsala ce da ke ta qaruwa a wannan lokacin. Maganinta a yau bai wuce kawai mutane su kula ba, su kiyaye a lokacin da suke bin hanyoyin da abin ya fi faruwa ko kuma su fara daukar doka a hannunsu. Na fadi haka saboda babu maganin matsololi guda biyu wadanda ke jawo matsalar.

Ta farko, a Kano muna da dubban yaran da ke yawo a titi, kuma su ke kwana a kangwaye, ɓiki, ƙarƙashin gada, kasuwanni da cikin tsofaffin motoci. Misali, in ka je bayan kamfanin Ajasa, hanyar shiga ‘yan siminti da ke gabas da titin Ibrahim Taiwo Road, akwai daruruwan yaran da ke kwana a cikin ‘stores’ da kantinan da Alhaji Aminu Dantata ya gina kuma ya yasar. A gurin za ka ga yara ‘yan shekara 9, 10, 11 zuwa 20 suna shan sholisho, wiwi, giya da duk abin maye. Sune ke irin wannan fashin a kewayen titin Ibrahim Taiwo Road.

Da yawancinsu gudaddun almajiraine, fitinannun yaran da suka gagari iyayensu, da irin shegun da mata masu bara suka haifa, tare da wadanda karuwan Railway suka haifa suka jefar. Police sun san da yaran. Hizba sun san da su. In ma an kama su, tunda ba iyayensu a kusa, ko kuma basu san iyayen ba, haka ake sakinsu su ci gaba da ta’annashi a gari!

Ba su kadai bane. In ka je Railway, Igbo Road by Market, IBB Road, Roundabout na Daula Hotel, Kano Guest Inn, bayan masallacin Idi na Kofar Mata, tashar New Road, Kasuwar Kurmi, Wada Head, Katsina Road, Kofar Mazugal, da sauran gurare, duka za ka samu irin wadannan yaran da ba su da gida sai titi, kuma ba mafad’i. Suna yawo da makamai kala-kala. Wallahi ko jakar kirki ka riqo, matuqar za ka bi ta irin guraren da yaran nan ke operation, kuma a lokutan da suke so, tabbas sai sun qwace!

Me gwamnati ya kamata ta yi a kan irin wadannan yaran? Wace gudunmawa al’umma za ta iya bayarwa wajen kawar da wadannan ɓata-gari?

Karin Labarai

Sabbi daga Blog