Gwamnan Borno, Zulum ya amince da daukan sabbin likitoci 594 aiki

Karatun minti 1

A kokarinsa na inganta asibitoci na fadin jahar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da daukan likitocin jinya a dukkanin asibitocin jihar.

Wakilin Dabo FM a Maiduguri, Ibrahim Mustapha ya bayyana cewa, cikin wani taro da gwamnan ya gudanar tare da shuwagabanni a fannin lafiya, Gwamna yace shakka babu Asibitocin kwaryar birnin Maiduguri suna da bukatan karin likitocin jinya, tare da na bangaren haihuwa.

Ya kara dacewa Gwamnatinsa bazatai kasa a gwiwa ba wajen kara likitoci a Asibitocin jaha tare da inganta wasu Asibitocin karkara.

Idan baku manta ba ko awatan ni dasuka gabata Gwamnati ta dauki tsofin likitoci wadda suka kammala aiki da niyar sake
mai do dasu aiki kasancewar sunsan aiki, dan haka Gwamnati tace zata tafi dasu tare da sake nuna wa likitoci sabi da suke
aiki yanayin aikin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog