/

‘Ran mumini fansa ne ga mutuncinsa Salallahu Alaihi Wa Sallam’

dakikun karantawa
  • Abubakar Salisu Sani (Bin Danladi Mailittafi)

A ƘADAMIN MUTUMTAKA, YANA CEWA DA SAHABBANSA: “Kaɗai dai cewa ni Mutum ne kamarku”

IDAN KUMA YA HAU ƘADAMIN MANZONCI, SAI YA CE DA SU: “A cikinku waye kamarni?” Ko: “Haƙiƙa ni ba kamarku ba ne”

Sanin hakan a bambance, a fahimce, a ladabce, ya sanya su da kansu, suna cewa da junansu: “A cikinku waye kamarsa?” Ko: “Ina mu ina Annabi (S.A.W)? Ko: “Mu ba kamar Manzon Allah (S.A.W) Ba ne” Ko: “Ba za a taɓa ganin kamarsa ba har abada.”

A ƙadamin Mutumtaka, har dutse yake ɗaura wa cikinsa saboda yunwa. Idan kuma ya hau ƙadamin Mursalanci, Ubangijinsa yana ciyar da shi, kuma yana shayar da shi (ba tare da cin wani abin ci, ko shan wani abin sha ba)
.
A ƙadamin Mutumtaka, da aka kira shi da Fiyayyen halitta, sai ya ce: ‘Ibrahimu ke nan.’ Ko ya ce: ‘Kada ku fifita ni a kan Musa.’ Idan kuma ya hau ƙadamin Risalanci sai ya ce: ‘Ni ne Shugaban ‘ya’yan Adamu… Adamu da waninsa suna ƙarƙashin Tutata.”

A ƙadamin Mutumtaka, yana tattaki da ƙafa, yana hawa jaki, ko doki. Idan kuma ya hau ƙadamin Annabta, sai ya keta hazo ba a jirgin sama ba, a kan Buraƙa.

A ƙadamin Mutumtaka, yana karɓar bashi, ko ya yi Kwanan-annabawa. Idan kuma ya hau ƙadamin Mursalanci, kyautar da komai yake yi na daga zakka, ko kyauta, ko sadaka, an yi masa tayin ko a mayar masa da dutsen Uhudu zinare ya ce, a’a.

A ƙadamin Mutumtaka, mutane suna cutar da shi, har ya cigita, waye zai masa maganin wane? Idan kuma ya hau ƙadamin Mursalanci, mala’iku suka zo rama masa, sai ya ce a’a, babu komai, ya yafe.

A ƙadamin mutumtaka, yana fatan ina ma ya haɗu al’umarsa da za su zo bayan wafatinsa. Idan kuma ya hau ƙadamin Manzonci, sai da izininsa Malakul-Mauti ya ɗauki ransa.

Rayuwarsa tana gudana ne ko dai a bisa ƙadamin Mursalanci, ko kuma a bisa ƙadamin Mutumtaka. Babu shakka Mutum ne shi, amma wane irin mutum? MUTUM NE MANZO. BASHARAN RASULAN (17:93)

Ran_Mumini_Fansa_Ne_Ga_Mutuncinsa S.A.W

Karin Labarai

Sabbi daga Blog