(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ganduje ya amince a zartar da hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi S.A.W

Karatun minti 1
Kwabid19 Ganduje
Dr Abdullahi Umar Ganduje - Gwamnan Kano sanye da takumkumi.

[AN SABUNTA] Rahotanni sun bayyana gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje  ya amince da rattaba hannu kan dokar hukuncin kisa da kotu ta yankewa wani mawaki da ya yi batanci ga fiyayyen halittu, Annabi Muhammad SAW.

Rahoton da Dabo FM ta tattara ya bayyana gwamna Ganduje, wanda ya dawo jihar ranar Litinin, ya tabbatar da yana goyon bayan hukuncin da kotu ta yanke, kuma ya shirya tsaf domin sanya hannu kan a zartar da wannan hukunci ba tare da bata lokaci ba.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Abba Anwar ya fitar da yammacin Alhamis bayan taro da gwamnan ya gabatar a gidan gwamnatin jihar Kano.

“Bazan bata lokaci wajen rattaba hannu akan wannan hukunci da kotu ta yankewa wanda ya yi batanci ga Annabin mu mai girma ba.” inji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Idan baku manta ba kotun shari’ar musulinci ta yankewa mawaki, Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan tabbatar da samun sa da laifin batanci ga Annabi SAW, wanda ya watsa a kafar Whatsapp a Mayun 2020.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog