1
Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu sabon kwamishinan ta bayan da CP Muhammad Wakili yayi ritaya daga aikin dan sanda bayan cikarshi shekaru 60 a duniya.
Babban siftan ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamau ya bada umarnin nada Ahmed Iliyasu a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kano.
Mai magana da yawun rundunar, DCP Frank Mba ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya fitar a babbar hedikwatar rundunar dake tarayyar Abuja.
