An kama Malamin makarantar allo da yake yin Luwadi da bayar da hayar ‘Almajirai’ don ayi dasu a Sokoto

Daliban wata makarantar allo a unguwar Arkilla dake jihar Sokoto sun tabbatar da malaminsu, Murtala Mode, yana tursasa yin luwadi dasu.

Daliban da shekarunsu ya kama da 4 zuwa 15, sun ce malamin yana kuma karbar kudade daga wajen wasu mutanen wajen domin tura musu yaran tare da yin luwadi dasu ta karfi da yaji.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito malamin, Murtala Mode ya amsa laifin tursasa daliban nasa wajen yi musu luwadi ta karfi da yaji, sai dai yace yara uku kawai ya taba tursasawa domin yin luwadin dasu.
Yara 6 ne dai suka tabbatar da malamin yana musu ta karfi wajen yi musu luwadin.

Da yake bayanin, Malamin makarantar allon, Murtala Mode, yace kaddarar Allah ce tasa hakan ya faru.

DaboFM ta tattaro cewa, a ranar Litinin 27/05/19, kwamishinan ‘yan sandan jihar SOkoto, Ibrahim Kaoje, yace ranar22 ga watan Mayu, wani lauya dake aiki da hukumar kare hakkin bil’adama ne ya kai karar malamin zuwa ofishin ‘yan sanda dake Arkilla, daga nan ne aka tisa keyarshi zuwa shedikwatar ‘yan sandan jihar.

Kwamishinan yace daliban mafi yawa daga cikinsu sun fito ne daga jihar Zamfara, inda ya tabbatar da Malamin ya mayar da yaran kamar karuwai mara ‘yanci kafin hukumar kare hakkin ‘dan adam ta kai kararshi.
Yayi kira ga iyayen yara dasu dena saka ‘yayansu a makarantun allon da basa kusa dasu.

Daily Nigerian ta gano cewa ‘yan sandan sun rufe makarantar allo a shirin da suke na mayar da dukkanin daliban gaban iyayensu.

Yara daliban guda 6, suna karkashin kulawar wani kungiyar kare yara inda kuma kungiyar lauyoyi musulmai ta Najeriya reshen jihar Sokoto take ciyar dasu.

%d bloggers like this: