0
Gidan Talabijin na Arewa24, ma shiryan shirin Dadin Kowa da Kwana Casa’in sun bude kafar neman jarumai domin taka rawa a sabon shirinsu na Kwana Casa’in.
Sanarwar ta fito daga hannun daya daga cikin mashiryan shirin, Salisu T Balarabe.
Mai neman shiga cikin shirin, zai tura Suna, Hoto, Shekaru da Adreshi zuwa ga adreshinsu na EMail a info@arewa24.com
Za’a rufe karbar sakonnin kafin ranar 31 g watan Mayun 2019.
Sanarwar tace, akwai ka’ido da tsarudda da mai neman taka rawa zai kasance yana da su kamar haka;
- A kasance ana jin yaren Hausa.
- A kasance ana da isasshen lokaci daukar shirin tare da gwaji.
- Damar yin tafiye-tafiye.
- Babu tarihin aikata laifi a baya,
Tashar tace zasu fara tantancewa a ranakun Asabar da Alhamis na watan Yuni, 2019. Asabar 8 ga watan, Alhamis 13 ga watan.
