Cristiano Ronaldo, dan wasan gaba na kungiyar Juventus, ya jefa kwallaye 3 a wasan farko da ya buga a sabuwar shekar 2020.
Wasan gasar Serie A da kungiyar Juventus doke kungiyar Cagliari da ci 4 da nema a ranar Litinin, 6 ga watan Janairun 2020 a filin wasa na Allianz Arena dake birnin Turin na kasar Itali.
DABO FM ta tattaro cewar Cristiano ya ne ya fara jefa kwallo a minti na 49 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
A minti na 67, Ronaldo ya kara jefa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, mintuna na 81, dan wasa Gonzalo Higuain ya jefa ta 3.
Minti na 82, Ronaldo ya jefa kwallonshi ta 3 wanda ya kama Juventus ta jefa kwallo ta 4.
Juventus tana kan mataki na 1 a teburin gasar Serie A ta kasar Italiya da maki 45 yayin da mai biye mata baya, Inter Millan, take da maki 42 da wasa daya a hannu.
