Labarai

Gwamnan jihar Niger ya siyo wa shuwagabannin kananan hukumomi sabbin motoci

Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, ya baiwa shuwagabannin kananan hukumomin jihar guda 25 sabbin hotoci kirar Hilux domin taimaka musu wajen tafiyar da ayyukansu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kungiyar kwadagon jihar ta bashi wa’adin kwanaki 21 domin fara biyan sabon albashin N30,000.

Da yake basu motocin, gwamnan yace motocin zasu taimaka musu wajen yun zurga-zurga musamman a wuraren da wahalar shiga a cikin garuruwan da suke shugabanta, kamar yacce Daily Trust ta tabbatar.

“Yawancin kananan hukumominmu cike suke da kasa. Muna sa ran zasu rika kula da abubuwan dake faruwa a wuraren da suke. Ina fatan wannan zai tamakawa musu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.”

Karin Labarai

UA-131299779-2