//
Sunday, April 5

Taskar Matasa: Abbas Nabayi, matashi mai zanen da yafi hoton kyamara

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A cigaba da shirin DABO FM na binciko hazikan matasan Arewa wadanda suke da baiwa a fannoni daban daban, yau mun zakulo wani matashi da yake zane mai ban sha’awa da mamaki.

Abbas Haruna Nabayi, dan shekara 21, dan asalin jihar Jigawa, mazaunin jihar Kano, ya kware wajen zane ta hanyar amfani da fenciri ba tare da sanya kala ba.

Masu Alaƙa  Hoton 'soyayya' na Baturiyar Amurka da dan Kano a dakin Otal ya janyo cece kuce

DABO FM ta tattara cewar Abbas Haruna Nabayi, yakan karbi wasu ‘yan kudade daga wajen mutane, ya zana su domin samun kudaden shiga.

Zuwa yanzu matashin ya zana wasu daga cikin manyan mutanen arewa hadi da sanannu ‘yan wasan kwallon kafa dana kwaikwaiyo, wadanda suka hada da Alhaji Aliko Dangote, Haj Aisha Buhari, Ahmad Musa da Aishatul Humaira.

Ga wasu daga cikin hotunan zanen Abbas Nabayi na shekarar 2019.

Zanen Abbas Nabayi
Dukkanin Hotunan mallakar Abbas Nabayi ne, DABO FM ta yi amfani dasu bisa sahalewarshi.

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020