Kungiyar Bayern Munich ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai bayan ta zura wa Kungiyar PSG kwallo daya a raga.
Dan wasa Coman ne ya jefa wa kungiyar kwallon guda daya tilo da ta bai wa kungiyar Munich damar daukar kofin a karo na 6 a minti na 59.
Wannan ne karon farko da kungiyar PSG ta kasar Faransa ta buga wasan karshe a kofin Zakarun bayan da ta haura matakin da aka saba cire ta na wasan gaf da na kusa da na karshe.