Jaipur India
A kasar Indiya, wasu daga cikin mabiya addinin Hindu sun bayyana fitsari da kashin Saniya a matsayin rigakafin kamuwa da cutar Corona.
Hakan yasa wasu dayawa daga cikinsu suka shirya taron wanka da kashin tare da shan fitsarin Shanu kamar yadda DABO FM ta shaidawa idanunta.
DABO FM ta tattara cewar ba sabon abu bane shan fitsari da cin kashin Saniya a Indiya ba, kuma mabiya addinin suna yin hakan ne saboda daraja da girmama Saniya da addininsu na Hindu sukace ya koyar.
Wani daga cikin masu rajin kare addinin Hindu, Om Prakash yace; “Itama Corona wata nauyin cuta ce ta Bacteria dake cutar damu duka. Kuma dama fitsarin Saniya yana magance duk wata ‘bacteria’.
Sai dai masana kiwon lafiya sun bayyana Corona a matsayin ‘Virus’ ba ‘Bacteria’ ba.
“Mun jima muna wanke kayayyakin gidajenmu da fitsarin domin tsaftace jikinmu dama zukatanmu. Ina da tabbacin fitsarin zai kare mu daga wanna cutar.”
Shima wani mai irin wannan ra’ayin mai suna Hari Shankar Kumar yace zargi gwamnatin kasar Indiya da rashin bayyana fitsarin Saniyar a matsayin maganar Corona bisa sonsu da shigowa da maganin kasashen waje cikin kasar ta Indiya.
