Labarai

Shinshina sarautar Waziri: Muhamad Nasir, Waziri Murabus yayi wa sabon Sarki mubaya’a

Sheikh Muhammad Nasir, waziri mai Murabus ya kaiwa sabon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar mubaya’a, wanda bayanai ke nuna cewa “ya fara neman a dawo dashi sarautar Wazirin Kano.”

A ranar Litinin ta cikin makon da muke ciki, Wazirin Kano ‘Murabus’ ya kai ziyara fadar Kano domin jaddada goyon bayanshi ga Alhaji Aminu Ado Bayero.

Majiyar DABO FM daga cikin gidan dabo ta tabbatar da cewa akwai shirye shiryen tube rawanin wazirin Kano, Malam Sa’ad Shehu Gidado a maye gurbinsa da Sheikh Muhammad Nasir ‘Wazirin Kano Murabus, babban aminin marigayi Sarki Ado Bayero kuma limamin masallacin waje.

Idan ba’a manta ba kafin rasuwar mai martaba Ado Bayero,ya nada limamin masallacin waje, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad a matsayin Wazirin Kano wanda gwamnatin Engr Rabi’u Kwankwaso taki amincewa da nadin har ma ta rahotanni suka bayyana yadda gwamnatin ta rushe wani sashin kofar malamin a shekarar 2014.

Dukkanin majiyoyin DABO FM daga fadar Kano da fadar Waziri Kano tayi nuni cewar “Masarautar Kano zatayi amfani da damar ta a wajen gwamnatin jihar Kano da aminantaka dake tsakanin Sarki Ado Bayero da Limamin waje domin dawo masa da mukamin da ake tube na Wazirin Kano.”

UA-131299779-2