Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar Talamiz, ya amince da a gabatar da Sallar Idi a fadin jihar tare
Kwanaki kadan suka rage ranar da aka ware a addinin Musulunci domin gabatar da Sallar Idi karamar da ta nuna karshen watan azumi na Ramadan.
A jawabin gwamnan yayi a ranar Talata a fadar gwamnatin jihar, yace dole ne wadanda aka aminta su halarci Sallar Idi su kasance masu yin da’a da sharudan da suka hada da bada tazara tare da amfani da kayyakin kariya domin gudun daukar cutar ta Kwabid19.
Sai dai gwamnan yace za a gudanar da Sallar ne babu kananan yara da mata, yayin da yace Maza majiya karfi kadai gwamnatin ta bai wa damar gabatar da Sallar Idi.
Kazalika, wakilin gidan Rediyon Freedom na jihar Jigawa, ya rawaito cewar gwamnan yace gwamnatin ta samar da gadaje 450 da za a kula da wadanda suka kamu da ciwon a fadin jihar.
