Aisha Solanke
Babban Labari Labarai

Akwai damuwa game da salon yaki da Korona a Najeriya – Amina Salanke

Shugaban kungiyar mata musulmi ta Federation of Muslim Women Association (FOMWAN) a turance rashen Zariya a Jihar Kaduna Hajiya Amina Abdulkadir Salanke, ta kwatanta biyayya da al’umma suka yi domin bin umarnin gwamnati da na masana kiwon lafiya domin dakile yaduwar cutar sarkewar numfashi ta Covid-19, a matsayin bin umarnin Allah da ya shimfida na a bi Shi da Manzon sa da kuma wanda aka sanya su zama jagorori.

Ta bayyana haka ne sa’ilin wata tattauna da ta hada ta da Dabo FM a Zariya.

Ta ce, zaton da ake na bin ka’idar gwamanti da na masana kiwon lafiya shi ne ya takaita yaduwar cutar, to amma akwai damuwa game da salon matakin.
Kuma ya kamata a ce shuwagabanni sun lura game da duk wani mataki da za su dauka kasancewar komai an tsara shi a addinan ce.

A cewar ta, Najeriya ma da ake damokradiyya, ya kamata a ce an lura da hakkin al’umma da ake mulka domin ta haka ne kowwa zai gane amfanin mulkin damkoradiyyar.

Ta bukaci mahukunta su rika sanya kishin addini da al’umma a ransu fiye da komai. Saboda ta haka ne ma za su samu nasara a dukkanin abun da suka sa ma gaba.

Ta kwatanta matakin da ilimin Najeriya ke ciki a yau a matsayin abun tashin hankali, domin tsawon lokacin da za’a dauka kafin ceto shi daga halin da yake ciki.

“Halin da ake ciki, abu ne da ya kamata gwamnati ta yi godiya ta kara gane cewar al’umma na tare da ita kuma tana yi mata biyayya dai-dai gwar-gwado. Kuma ta yiwa Allah ta sassauta akan matakin da take kai domin baiwa Jama’a daman walwala”, Inji Amina Salanke

Ta kara bayyana yadda koda yaushe suke kara samun korafi daga mata da suke zaune a gidajen aure game da halin kuncin da suka shiga saboda kullen da aka yi, a matsayin abin kaice da takaici.

Kuma daga karshe ta roki Allah ya kawo sauki a halin da al’umma a fadin duniya ke ciki.

Karin Labarai

UA-131299779-2