1
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai yace ya yafewa malaman da yace suna zaginshi i akan dokar fita a jihar Kaduna.
DABO FM ta tattara cewar malaman addinai a jihar Kaduna sunyi ta sukar El-Rufa’i akan dokar hana fita da suka ce ta hana su salla musamman ta Juma’a.
A jawabin da gwamnan yayi a yau Talata, yace gwamnatin jihar za ta cigaba da daukar dukkanin matakan kariya daga cutar Kwabid19 da ta addabi duniya.
“Ko a Makka ba za a yi sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani. Saboda haka Allah ya isa.”
Sai dai yace ba zai yafewa dukkanin masu yi musu kazafi ba.
