RAJASTHAN: Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta bayyana cafke mutane 97 bisa zuwa gidan rawa na dare da ake kira ‘Night Club’ a jihar Kano duk da dokar zama gida da gwamnatin jihar ta sanya domin dakile yaduwar cutar Kwabid19.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
DSP Haruna ya ce rundunar ta samu bayanai a ranar 6 ga Yuni cewar wasu mutane sun taru su na cashewa a gidajen rawar Otal din Mozida da ‘CLub 47’ da suke a Sabon Gari, cikin birnin jihar Kano.
Ya bayyana cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Habu Ahmad ya bayar da umarnin kamo mutanen bayan samun bayanan.
“Mun kama mutum 97 da suka karya dokar hana taruwa waje guda tare da zuwa gidan rawa a lokacin da dokar hana fita take aiki.”
Kazalika, DSP Haruna Abdullahi ya bayyana cewar wadanda suka sun hada da mata 40 da maza 57 tare da shugabannin dake kula da gidajen rawar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ ya rawaito.
“Mun aike masu laifin zuwa kotu domin karbar hukunci.”
