Home LabaraiZa mu kurmushe ‘yan bindiga kafin lokacin damuna – El Rufa’i

Za mu kurmushe ‘yan bindiga kafin lokacin damuna – El Rufa’i

by Dabo Online
0 comments
El Rufa’i

RAJASTHAN: Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewar kafin lokacin damuna, zasu shafe ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’addar.

Gwamnan ya bai wa manoma tabbacin cewar za su yi noman damunarsu ba tare da fargabar ta’addancin ‘yan binduga a fadin jihar Kaduna ba.

Gwamnan ya bayar da tabbacin ne yayin da yake raba wa manoma takin shekarar 2020 da Ma’aikatar Gona ta Najeriya ta bai wa manoma domin yin noman damuna.

“Za mu cigaba da tabbatar da nemawa gonakin al’ummarmu tsira ba tare da matsala ba.” Ya ce gwamnatin za ta shafe kafatanin ‘yan binduga domin tabbatar ga zaman lafiya ga daukacin al’ummar Kaduna.

“Ba za mu tattauna da su ba, cikin izinin Allah za mu shafe su baki da ya cikin wani shirin hadin gwiwa da Rundunar Sojin Sama, Sojin kasa da Rundunar ‘Yan Sanda.”

“Mu na aiki tukuru domin ganin mun gama da ‘yan bindugar nan kafin lokacin damuna ya kankama.”

DABO FM ta tattara cewar gwamnan ya bai wa al’ummar Kaduna musamman al’ummar kananan hukumomin Igabi, Giwa, Birnin Gwari, Kajuru da Chuku inda ‘yan bindigar suka addaba, ya bayar da tabbacin mai do da zaman lafiya da cigaba da rayuwa a yankunan kamar yadda ake yi a baya.

“Za mu tsayar da ta’addancin nan ko kuma duk su mutu, za mu kashe su duka kuma babu tuba ko neman gafara akan haka.”

Daga karshe gwamnan ya yaba wa shugaba Muhammadu Buhari bisa tsarin kyautata ayyukan noman da yace yana yi a Najeriya.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00