RAJASTHAN: Wata tsohuwa mai shekarun haihu 75 a duniya ta fada rijiya a unguwar Tudun Wuzurchi dake cikin kwaryar birnin Kano.
Tsohuwar da aka bayyana da sunan Hajiya Zuwaira Kabir ta fada cikin rijiyar ne a yayin da take diban ruwan rijiyar a ranar Litinin.
Shugaban hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Sa’idu Muhammad ne ya tabbatar da faruwar al’amarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ya shaida cewar; “Tsatsauyin fadawa rijiyar ya ritsa da matar ne a lokacin da take kokarin diban ruwa a cikin rijiyar da misalin karfe 5:45 na asubar ranar Litinin.”
Sai dai ya shaida cewar jami’an hukumar sun samu nasarar ceto matar bayan sun samu kiran gaggawa daga masu neman dauki.”
“Jami’anmu sun samu ceto matar.”
“Mun samu kira mai dauke da matsanancin hali daga wani Mallam Musbahu Sani dake unguwar Tudun Wuziurchi a Kano da misalin 5:45 na asuba kan cewar wata mata ta fada cikin rijiya.”
“Bayan mun samu kiran, mun yi gaggawar aike da jami’an domin kai dauki kuma sun samu nasarar ceto ta.
Daga karshe jami’in ya yi kira ga al’umma da su rika rufe rijiyarsu tare da yin gini mai tsawo a kewayen rijiya musamman saboda kariya ga kananan yara, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito.
