1
Sabon shugaban riko na jami’iyyar APC, Ajimobi ABiola ya na nan da ranshi cikin koshin lafiya, babban mataimakinsa a fannin yada labarai, Bolaji Tunji ne ya tabbatar da haka.
Kazalika wasu daga cikin makusantan Ajimobi sun tabbatar da cewar yana nan a raye.
Hakan na zuwa bayan wasu kafafen sadarwa suka fitar da labarin mutuwarshi da daren yau Alhamis.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa Ajimobi Abiola yana cikin halin matsananciyar rashin lafiya da ta kai ga anyi masa aiki a yau Alhamis wanda har yanzu bai farka ba, DABO FM ta tabbatar.
Kazalika Likitoci sun tabbatar da cewa zuwa yanzu Ajimobi ba ya dauke da cutar Kwabid-19.
