0
A shirin takaitacciyar nasiha na DABO FM, mun tattaro muku sharrin mutane masu fuska biyu daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Mafi sharrin mutane shi ne mai fuska biyu.
Manzon allah saw ya ce: Za ka sami mafi sharrin mutane a wajen Allah ranar alkiyama, shi ne mutum mai fuska biyu, ya je wajan wadancan da wata fuska, ya je wajen wasu da wata fuska daban.
Bukhari. 5711. Da muslim 2526. Suka ruwaito.
Wannan zamani, masu fuska biyu sun yi yawa. A Addini, Siyasa da mu’amalar zamantakewa.
Allah ya kyauta.
