ZAMANTAKEWARMU.
Wani abu da sau da dama yake Sosa zuciyar duk wani mai kunya da sanin yakamata shine, yanda sau da dama akan tituna ko jikin shataletale da bakin kasuwanni, za ku ga mutane sun yaye jiki suna kama ruwa ko bayan gida.
Wannan dabi’a ba karamar mummunar aba ba ce, hakanan shari’ah ta kyamaci hakan nesa ba kusa ba.
Abin takaicin shi ne, irin wadannan mutane sau da yawa suna yin kasuwanci ko hada-hada a wadannan wurare. Hakan kadai ya zama babban kalubale ga lafiyarsu. Domin iska za ta iya kwaso cututtuka ta kawo musu su shaka. Ko ma kudade su debo cutuka su zuba a cikin abinci da dai sauransu.
Abin lura dai shine, akwai hanya daya da dama da za su iya yin bandaki domin biyan bukatarsu. Dan kudi da za su hada da bai kai ya kawo ba, za su iya yin hakan don kare mutuncinsu da lafiyarsu.
Daga karshe wani yunkuri da gwamnatin tarayya ta ke yi don ganin wadannan wurare na biyan bukatu zai taimaka sosai don raguwar wannan matsala. Kuma a karshe za a kai matsayin duk wanda aka kama yana yin waccar dabi’a mara kyau zai iya fuskantar hukunci.
