/

Jayayyar hukuncin Kisa da satar Sadiya Idris gami da sauya mata addini -Daga Hassan Ringim

dakikun karantawa

Tun bayan da kotun shari’ar musulinci ta yankewa wani mawaki da ya zagi fiyayyen halittu, Annabi Muhammad SAW mutane da dama suka shiga mahawara mai zafi kan dacewar hukuncin, sai dai kuma maimakon a sanya wata matsala dake da muhimmanci ta yarinya ‘yar shekara 11 da wani Fasto ya sace ya canja mata addini a gaba amma abin takaici anbar jaki ana dukan taiki, wakilin mu Hassan Ringim ya yi mana jan hankali akai.

Har yanzu dai da yawa daga cikin ma’abota ilimi kususan daga yankin Arewa sun ma kasa fahimtar ainahin matsalar da ke ciki gaba da yi mana ta’adi a sirrance, irin yanda kame da garkuwa gami da sauya addinin ‘ya’yan Musulmai ba.

A ranar Laraba kafar Dabo FM buga labarin yanda wani fasto mai suna Juna ya garkame wata Musulma Sadiya Idris, tsawon shekaru 7, lamarin da ta kai jallin mahaifinta ya mutu saboda kunci sanadin jininsa da ya hau.

Kamar yanda wakilin Muhammad Makama ya labarta labarin, dole zuciyar mutum ta sosu, kuma a fahimci muna cikin tsaka-mai-wuya.

Abin da ya ke bani mamaki da takaici shine, sai ku ga Musulmai sun hadu suna ta kwafsa musu akan wani abu da ba zai zama mafi a’ala a wannan yanayi da muke ciki ba, da sunan addini.

Amma kuma a daya bangaren sun yi buris da yanda ake lalata addinin muslunci a fakaice, kuma wannan ta’adi shine idan ya yi yawa sai ma a wayi gari a rasa da me za a kawo gyara.

Batun sabani ko fahimta ba sabon abu ba ne a addini. Don ko a gaban Annabi Muhammad SAW sahabai kan yi sabani akan wasu lamura da suka rayuwarsu da ibadu, amma hakan ba ya haddasa su shagala wajen ganin sun yaki gami da Hana kafurai da munafukai sakat a lokutan da bukatar hakan ta taso.

Dole ne kowa ya gane cewar da ace wani Musulmin aka samu da kuskuren daukar wata kirista hakan ta faru, to da har CNN sai sun buga labarin, dama ba a zancen cikin gida Najeriya.

Ya kamata mu fahimci halin da muke ciki, mu zamo masu kare hakkin juna da kuma tunkarar duk wani makiyin zahiri da badini. Akasin hakan kuwa, wallahi za mu ci gaba da yin asara gami da jin kunya tare da fuskantar kalubale iri-iri da za su zamo mana alakakai.

Ba wanda ya isa shi kadai ya sauya wani hukunci ko fatawa a shari’ance a yau din nan, amma mutum daya zai iya dakile barnar da za ta iya illata Musulmai dubu a Najeriya. Allah Ya shiryemu Ya sa mu gane gaskiya da kuma bin ta, amin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog