/

Goron Juma’a: Murmushi dabi’ar kwarai

Karatun minti 1

 

Abin lura:
Duk da rasuwar dukkanin ‘ya’yanshi (SAW) illa Nana Fadima R.A!!

Duk da rasuwar matar shi ta fari kuma mahaifiyar ‘ya’yanshi!!

Duk da kasancewarshi maraya gaba da baya tun daga ƙuruciya!!

Duk da rasuwar makusanta kuma masoya a gare shi Hamza R.A, Ja’afar R.A ga baffanshi Abu Dalib!!

Duk da irin ɗumbin nauye-nauyen da suke kan shi na al’umma wajen yaɗa kalmar Allah da kawo gyara a cikin al’umma da kuma fama da mushrikai da kaidinsu!!

Amma bai kasance ba illa mai yawan murmushi da fara’a!!
Wannan shine Manzon rahma sallallahu alaihi wasallam.

Kayi murmushi domin koyi da abinda yake yi, sannan kuma ka dace da samun lada na sadaka, kamar yadda Manzon Allah S.A.W yace: ((Murmushin ka ga fuskar ɗan uwanka sadaka ne)).

Kuyi murmushi ya bayin Allah.

-Edreez Abdulaziz Sani

Karin Labarai

Sabbi daga Blog