Wace irin Riba ka ci a rayuwarka? Dage da Hassan Ringim

dakikun karantawa

Wani zai iya yin matukar mamaki idan aka tareshi gami da yi masa tambayar ‘shin daga balagarka zuwa yanzu wace riba ka ci a rayuwarka?

Wata kila zai yi kokari ya ga ya lissafo tarin nasarorin sakamakon da ya samu idan a Boko ya ke, wani kuma ya nusar da cewar jarinsa a kasuwa ya kai kaza, akwai wanda zai bugi kirjin ya mallaki abu kaza da kaza na kyale-kyalen duniya da sauransu. Wata kila wata za ta iya cewar ta samu sa’a an mata aure ta haifi yara kuma ta na zaune kalau da Mai Gida gami da yara…. Amma shin wadannan duk nasarorin lissafawa ne?

Duk wani abu da mutum zai mallaka na duniya, ko ya yi, ko ma ya ji yana tare da shi a cikin rayuwarsa, to miliyoyin dubunnan mutane sun samu hakan shekaru marasa adadi da suka shude. Ba wani abu da mutum zai yi tutiya da shi a yau, ba tare da an samu wanda ya samu fiye da shi a wani zamani da ya shude a duniya ba. Shin don wani ya samu fiye da na shi, sai a ce shi bai samu wata nasara ko riba ba?

Amsar ita ce ribar da aka samu ta wane mizani za a kalleta, hakanan menene tasirinta a rayuwar wanda ya mallaketa tun yana raye har zuwa lokacin da za a busa kaho?
Wadanda suke ganin sun mallaki karatu mai zurfi, shin wace rawa ya taka a gudanawar rayuwarsu? Dan kasuwa da me zai kalli ribar da ya samu gami da bunkasar kasuwar ko da bayan an tsaya domin a yi hisabi ne? Ita wacce ta tara yara ga Mai Gida, ya za ta fassara rawar da suka taka mata kasancewar akan mizanin amana suke ita da yaran?

Wani zai iya dariya ya ce, to ya kenan mutum zai fuskanci gami da bayyana ribar da zai yi tutiyar ya mallaka?
Amsar ita ce, tun da farko ka tabbatar an yi komai na komai a duniya kafin zuwanka. Don haka komai da zai zamo maka komai, ya zamto ya kasance wanda za ka yi alfahari da shi ranar tsayuwa(Hisabi)
Duk wata ribar rayuwa da za ta jefa mutum ga halaka, abar nadama ce a ranar da ba wanda zai iya kirga ribar kowa wacce ya samu a duniya kafin mutuwa!

Karin Labarai

Sabbi daga Blog