Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta sanar da cewa za a daina buga fasfo a wasu cibiyoyi guda 10 na hukumar da aka ɗade ana aikin buga fasfo.
Hukumar ta ce daga 10 ga watan Agustar 2026, za a rufe ayyukan cibiyoyin, za kuma a mayar da ayyukansu zuwa babbar cibiyar buga fasfo ta hukumar da ke birnin tarayyar Abuja.
Sanarwar na ƙunshe a cikin wata takarda da hukumar ta fitar mai lamba NIS/HQ/DCG/POTD/6124/43 ɗauke da sa hannun T.O Olaiya, babban mataimakin shugaban hukumar mai kula da sashin fasfo da takardun tafiye-tafiye.
Za a rufe dukkani cibiyoyin fasfo guda biyu da ke Kano, cibiyoyin da ke Farm Center da kuma Dawakin Kudu.
Sauran cibiyoyin da za a daina ayyukan sun hada da cibiyar hukumar ta garin Jalingo a jihar Taraba, Cibigar jihar Gombe, Yola Adamawa, Bauchi.
Sai kuma cibiyoyin jihar Rivers, Akwa Ibom, Bayelsa da kuma Cross Rivers.
