15
A dai dai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar cin zabe karo na biyu, matasa daga bangarori daban daban musamman mutanen arewa sun nuna farincikinsu ta hanyoyi daban daban.

Bala Haruna
Jaridar Independent ta rawaito cewa, matashi Bala Haruna, wanda yayi wanka a cikin kwata har na tsawon mintuna goma tare da kwankwadar ruwan ya rasu. Tin bayan da matashin ya sha ruwan kwatar ne ya kamu da rashin lafiya.
Lamarin daya saka aka garzaya dashi asibiti domin karbar agajin gaggawa.
