‘Yan takarar shugaban kasa 39 sun roki Atiku ya janye kudirin zuwa Kotu

Karatun minti 1

Daga cikin ‘yan takarkaru kusan 100 da suka nemi tsayawa shugabancin kasa Najeriya, 39 daga ciki sun bukaci dan takarar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya janye kudirinshi na zuwa kotu.

Da yake magana, shugaban jami’iyyar APDA, Shittu Muhammad yace bai kamata dan takarar dama jami’iyyarsa ta PDP suki amincewa da wannan sakamakon zaben ba.

“Duk da cewa yana da damar zuwa kotu, amma kamata yayi ya hakura domin ciyar da dimokradiyya kasa gaba.”

“Lokaci yayi daya kamata mu manta da komai, ku dawo wajen nemawa kasar mu mafita tare da fatan alheri ga wadanda suka sami masara.”

“Shugaba Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar duk ‘yan uwa ne, ina kira ga Atiku ya janye kudirinshi na zargaya kotu, duba da shawarwarin janyewa da manyan kasar nan suka bashi irinsu Gen. Ibrahim Babangida, Gen Abdulssalam Abubakar.”

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog