Copyrighted.com Registered & Protected

Bazan dena sukar Buhari ba, domin har yanzu yarona ne – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo yace bazai taba dena sukar shugaba Muhammadu Buhari ba har sai ya fara yin abu na daidai.

Obasanjo yace babu wata matsala tsakaninshi da shugaba Buhari, illa iyaka yanzu lokaci ne na dimokradiyya kuma yana da damar fadin abinda yake so indai gwamnati tayi kuskure.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo yayi wannan kalami ne bayan da Sarkin Egbaland, Oba Aremu Gbadebo yayi masa wata ‘yar togashiya a wajen taron murnar zagowar ranar haihuwar Obasanjo a garin Abeoukuta.

Sarkin yace bai kamata Obasanjo yana tsoma baki akan harkokin da suke gudana a kasa ba duba da irin yawan shekarunshi na haihuwa.

Da yake mayar da martani, Chief Olusegun Obasanjo yace bashida wata matsala shi da Buhari.

“Babu wani shugaba da za’ayi a Najeriya da zai dade a mulki kamar ni, nasan meye shugaban kasa, dole ne nayi magana idan naga anyi abu ba daidai ba.”

“Ya Sarki (Aremu), kana cewa Buhari mai gidankane, ni kuma Buhari yaro na ne. Bazanyi shiru ba har sai kacewa mai gidanka shima yayi shiru.”

 

%d bloggers like this: