Gwamnatin Zamafara zata dauki matsafa 1,700 domin tabbatar da tsaro

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdulaziz, tace zata dauki matsafa 1,700 domin samarwa jihar zaman lafiya.

Gwamnatin ta bayyana haka ne ta hannun Kwamishinan kananan hukumomi na jihar, Alhaji Bello Dankande, a wani taro da yayi da Sarakunan gargajiyar jihar.

“Kowacce masarauta zata samu mutum 100 hadi da 500 da muka dauka daga farko. Zamu girke wasu a gidajen mai domin hana ‘yan bindigar samun mai.

Yace Gwamnatin bazata lamunci a cigaba da tashin hankali a fadin jihar ba.

“Abin ya isa haka, bazamu bari a cigaba da wannan kisan kiyashi da akeyi a jihar mu ba.”

“Gwamnatin tarayya data jiha nayin iyakacin  kokarinta na yaki da ‘yan ta’addar.

A1A67A8C 6C64 4007 8DA8 874CCD0E0FE3 - Dabo FM
Daga Daily Trust

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00