Kano: Zaɓaɓɓun ‘yan majalissun PDP a jihar Kano sun karbi takardar shaidar lashe zabe daga INEC

NYau Alhamis, 04/04/19, zababbun ‘yan majalissun jihar Kano karkashin inuwar jami’iyyar PDP suka karbi shaidar lashe zabe daga hukumar INEC.

Hon Tukur Muhammad Fagge

Hukumar ta tsara baiwa dukannin ‘yan majalissun jihar Kano shaidar takardar lashe zabe a jiya Labara, sai dai hakan ya kawo tsaiko bisa bukatar PDP ga INEC domin chanza wa ‘yayanta ranar karbar takardar shaidar.

Hon Isiyaku Ali Danja

‘Yan majalissun guda 13 sun karbi takardar a babban ofishin hukumar dake cikin birnin Kano kusa da Hajj Camp dake karamar hukumar Fagge.

TALLA
Alhajin Baba, KMC

A kananan hukumomi 13 ne PDP ta samu nasarar lashe zaben yan majalissun jiha kawai.

Hon Musa Umar Gama, Nassarawa

Jami’iyyar PDP ta aikewa hukumar INEC takardar ta neman alfarmar zance ranar karbar takardar bisa abinda ta kira gudun kauweca hargitsi tare da shirin jami’iyyar APC na tada hargitsi.

Masu Alaƙa  Zaben Kano: Kotu ta amince da bukatar "Abba Gida Gida"

 

 

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.

%d bloggers like this: