0
Kungiyar kwallon kafa ta Valencia ta lallasa Barcelona da ci biyu da nema a wasan karshen na cin kofin Copa del Rey da aka buga da yammacin yau Asabar 25/05/2019.
Valencia ta jefa kwallon farko ta hannun dan wasanta Kevin Gameiro a minti na ’12, inda Rodrigo ya kara jefa kwallo a ragar Barcelona cikin minti na ’33.
Barcelona ta samu farke kwallonta daya tal ta hannun dan wasa Lionel Messi a minti na 73.
Valencia ce ta lashe kofin na kakar wasan 2018/19 ta bana.
Alkalin wasa Alberto Undiano na kasar Spaniya ne ya busa wasan da aka buga a filin wasa na Estadio Benito Villamarin.
