Siyasa

Goodluck Jonathan ya zama mai bawa gwamna shawara a harkokin Ilimi na jihar Bayelsa

Gwamnati jihar Bayelsa ta baiwa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan babban mai bada shawara a Asusun Cibiyar Habbaka Ilimi ta jihar Bayelsa.

Gwamnan jihar Seriake Dickson ne ya bayyana haka a wajen bude cibiyar a garin Yenagoa, babban birnin jihar.

Gwamna yace tsohon shugaban kasar shine zai rike cibiyar tare da sa ido akan yadda ake tattara kudin asusun cibiyar.

Dickson ya kara da cewa; Goodluck Jonathan ne kashin bayan cigiban Ilimin jihar Bayelsa bisa hubbasar da yayiwa bangaren lokacin da yake gwamnan jihar Bayelsa.

Majiyoyin DaboFM da Jaridar Daily Trust sun tabbatar cewa; Dr Goodluck Jonathan ya karbi aiki tare da alkawarin yin bakin kokarinshi wajen ciyar da Ilimi dama asusun jihar gaba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Da Turawa da abokan hamayyata (APC) akayi shirin wulakanta ni bisa rashin aminta da auren Madugo

Dabo Online
UA-131299779-2