(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ra’ayoyin Wasanni: Ko dama Aljanun Messi, Man Utd suka raina? Au ashe fa an daure Aljanu

Karatun minti 1

Ra’ayoyin Wasanni daga magoya bayan kwallon Kafa

Dan wasa Lionel Messi ya gaza tabukawa kungiyar Barcelona komai bayan da kakar wasanni bana tazo gangara.

Sai dai ma’abota kwallon kafa suna ganin ko dama kungiyar Man Utd, Lionel Messi ya raina? Duk lokacin da Lionel Messi ya hadu da United, yana buga wasan kece raini.

Messi yana kallo Liverpool tayi masa haramiyar buga wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turan da rabonshi da bugawa tin shekarar 2015. Messi yana kallon Liverpool ta zura musu kwallaye har 4 a Anfield amma ya kasa komi.

Sai gashi Valencia ma tayi masa haramiyar daukan kofin cikin gida na ‘Copa del Rey’, bayan data zabgawa Barcelona tsumagiya a filin wasa na Estadio Benito Villamarin.

Ko dayake dama sunanshi Aljani, kuma malamai sun fada mana cewa, da zarar watan Ramadana ya kama, ana daure aljanu.

Ko kuwa daman Messi, Manchester United kawai ya raina.?

Daga Aliyu Mai Kano Pillars.

Zaku iya turo da naku ra’ayoyin a adreshinmu na email

Danna anan don aiko mana da sako📧

Karin Labarai

Sabbi daga Blog