0
Alƙalin alƙalan jihar Yobe, Musa Nabaruma ya rasu a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja a daren ranar Litinin.
Kanin mammacin, Mustapha Nabaruma ne ya bayyana gidan Talabijin na Channels labarin mutuwar a ranar Talata.
Yace Alkalin alkalan ya rasu ne bayan fama da wata matsananciyar rashin lafiya da aka kwantar da shi a babban asibitin tarayya na Abuja.
Kafin rasuwarshi, ya kasance alkalin alkalan jihar Yobe na tsawon shekaru 9 tin daga shekarar 2011 da tsohon gwamnan Ibrahim Gaidam ya nada shi.
