RAsuwa Sheikh Dan Almaiji
Labarai

Ganduje ya nuna alhinin mutuwar shugaban limaman Juma’ar Kano, Sheikh Dan Almajiri

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna alhininshi ga mutuwar shugaban limaman Juma’a na jihar Kano, Sheikh Fadlu Dan Almajiri Fagge.

DABO FM ta tattara cewar malamin ya rasu ne a ranar Talata a unguwar Fagge, kamar yadda iyalan malaman suka bayyana.

Da yake aike sakon ta’aziyya, gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje ya bayyana rashin malamin a matsayin babban rashi ga al’ummar jihar Kano da ma Najeriya baki daya.

Cikin sakon da gwamnan ta fitar ta hannun mai magana da yawunshi, Abba Anwar, Ganduje yace; “Sheikh Dan Almajiri ya kasance malamin Musulunci mai kira ga zaman lafiya da kaunar juna wanda hakan ta sanya dalibansa sun zama abinda suke a yanzu.”

“Kasancewarshi malamin Musulunci wanda fahimtarshi da addini ya hadu da nagartattu halayenshi ya sa yake kasancewa mai fifito a cikin jeri. Sheikh Dan Almajiri mutum ne mai kan-kan da kai, mai mutunci da mutunta mutane tare da jinkai.”

Ganduje ya yi kira ga al’umma da suyi koyi da kyawawan halayensa wadanda suke kai wa ga samun rahama da jinkai a wajen Allah.

Daga karshe gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarshi ga iyalan malamin tare da fatan rahamar Allah a gareshi, ya roki Allah Ya kuma bai wa iyalanshi hakurin juriya.

Karin Labarai

UA-131299779-2