Allah Ya sa mutuwar mahaifin Kwankwaso ta zama silar daidaito a tsakaninsa da Ganduje -Muazu Magaji

Karatun minti 1
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiya Mu’azu Magaji ya yi addu’ar don samun daidaito tsakanin tsohon gwamna Kano, Rabiu Kwankwaso da gwamna Dr Abdullahi Ganduje na jihar Kano.

Tsohon Kwamishinan wanda yanzu shi ne shugaban kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa na aikin janyo bututun iskar gas zuwa jihar Kano ya yi wannan addu’a ce kwana 1 bayan rasuwar mahaifin Sanata Kwankwaso.

DABO FM ta tatara cewar Muazu Magaji ya ce yana fatan mutuwar mahaifin Kwankwaso ya zama silar shiryawarsu kamar yadda mutuwar mahaifiyar Ganduje ya zama daga cikin sanadin rabuwarsu, kamar yadda ya bayyana.

“Ya Allah, kamar yadda ka jarrabi bayinka da sabani a lokacin rasuwar mahifiyar Ganduje, Allah ka sa wannan rashi na nahaifin Kwankwaso ya zama silar daidaito tsakaninsu.”

Da alama maganar tsohon kwamishinan ta birge mutane musamman yadda ake ganinsa mai yawan yin maganganu da suke suke musu kallon sakin layi a kan al’amuran yau da kullin wadda ta kai ana masa lakabi da WIN-WIN Caji wasu kuma suce WIN-WIN Canji.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog